Karamar hukumar Birnin kudu ta jaddada kudurinta na cigaba da tallafawa al`amuran rigakafi a yankin

0 247

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Magaji Yusuf ya bada wannan tabbacin a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan al`amuran rigakafin cutar shan-inna wanda aka gudanar a dakin taro na sakatariyar karamar hukumar.

Haka kuma ya bada tabbacin karamar hukumar na bada cikakken hadin kai da goyon baya domin samun nasarar rigakafin cutar polio a yankin.

A nasa jawabin manajan hukumar lafiya a matakin farko na karamar hukumar, Malam Bello Abdulkarim yace kimanin kananan yara dubu dari da casa`in aka yiwa rigakafin cutar polio a yankin, a zagayen da ya gabata. Daga nan ya yabawa karamar hukumar Birnin kudu da shugabannin al`umma da na addini da sauran masu ruwa da tsaki bisa tallafawa al`amuran kiwon lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: