Kotun duniya taki bai wa Isra’ila umarnin tsagaita wuta a Gaza

0 140

Kotun duniya taki bai wa Isra’ila umarnin tsagaita wuta a ci gaba da yakin da ake gwabzawa a Gaza, sai dai ta bata umarnin daukar duk matakan da suka dace wajen ganin ta hana sojojin ta aikata kisan kare dangi a yakin dake ci gaba da gudana ba tare da kaukautawa ba.

Wannan hukunci ya biyo bayan karar da Afirka ta kudu ta shigar a gaban ta domin kawo karshen abinda ta kira kisan kare dangin da Isra’ilar keyi, sakamakon kai hare haren da ya hallaka Falasdinawa sama da dubu 25.

Yayin yanke hukuncin wanda ya dauke hankalin duniya, alkalan kotun sun baiwa Isra’ila umarnin hana sojojin ta daukar matakin aikata kisan kare dangin, yayin da suka ce a karkashin dokar majalisar dinkin duniya ta shekarar 1948 Falasdinawa na da kariyar da suke bukata daga kotun. Mai shari’a Joan Donoghue da ta jagoranci yanke hukuncin ta yi bayanai sosai a kan korafin da Afirka ta Kudu ta gabatar da kuma shaidu daban-daban da suka kunshi rahotannin hukumomin Majalisar dinkin duniya daban-daban a kan halin da ake ciki a Gaza da kuma yadda munanan hare-haren ke ritsawa da fararen hula tare da hana kai kayan agaji yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: