Gwamnatin tarayya za ta kaddamar da kwamitin da zaiyi  aiki kan mafi karancin albashin ma’aikata

0 202

Gwamnatin tarayya za ta kaddamar da wani kwamiti mai wakilai 37 da zaiyi  aiki kan mafi karancin albashin ma’aikata na kasa, tare da bayar da shawarwari kan karin mafi karancin albashi a kasa.

Wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ya fitar, ya bayyana cewa kaddamar da kwamitin na cikin umarnin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar na kafa shi.

Ranar talata aka shirya bikin kaddamar da kwamitin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A cewar sanarwar, Bukar Goni Aji, tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ne zai shugabanci kwamitin da mambobinsa daga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi da kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago.

A baya dai kungiyoyin kwadago sun sha tayar da jijiyoyin wuya kan sabon mafi karancin albashi ga ma’aikata a matakan tarayya da na jihohi.

Wannan dai ya biyo bayan hauhawar kayayyaki da aka fuskanta sakamakon matakin cire tallafin man fetur.

A watan yunin bara ne, shugabannin kwadagon sukayi kira ga gwamnati ta kara mafi karancin albashi daga naira dubu 30 zuwa naira dubu 200 domin dacewa da halin  tattalin arzikin kasa ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: