Za’a raba wa manoman rani man fetur kyauta

0 190

Gwamna Nasiru Idris na jihar Kebbi yace gwamnatin tarayya hadin guiwa da gwamnatin jihar Kebbi sun kammala shirye-shiryen rabawa manoman rani man fetur kyauta a matsayin tallafi domin bunkasa harkokin aikin gona a jihar.

Gwamnan, lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC a karamar hakumar Yauri a karshen makon nan, yace shi da Ministan kasafi da tsare-tysaren tattalin arziki Sanata Atiku Bagudu sun cimma matsayar yadda za’a samar da man fetur ga manoman rani. Gwamna Idris yace gwamnatin sa zata raba famfunan bayar da ruwa masu amfani da hasken rana dubu 12 ga manoma, yana mai cewa tuni su kammala raba guda dubu 6 kawo yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: