Kudirin kafa bankin cigaban ma’adanan kasa ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa

0 71

Kudirin kafa bankin cigaban ma’adanan kasa ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa.

Kudirin wanda Yakubu Oseni na jam’iyyar APC daga Kogi ta tsakiya ya dauki nauyinsa, na neman kara bunkasa zamantakewa da tattalin arziki mai dorewa.

Haka kuma ana kokarin inganta fannin ma’adanai da ingancin rayuwar al’umma ta hanyar samar da jarin kudade a fannin.

‘Yan majalisar dai sun kayyade kudi naira biliyan 500 domin kafa bankin.

An karanto kudirin dokar a karo na biyu bayan Yakubu Oseni ya jagoranci muhawara akai a jiya.

Kudirin, in ji shi, an samar da shi ne da nufin samar da kudaden da ake bukata na bangaren ma’adanan kasa a kasarnan.

Bayan kammala karatu na biyu, an mika kudirin ga kwamitin majalisar dattawa mai kula da ma’adanai domin bayar da rahoto nan da makonni hudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: