Majalisar wakilai ta umarci hukumar kwastam da ta biya naira miliyan 200 ga wasu mutane 10 da suka kashe
A halin da ake ciki, majalisar wakilai ta umarci hukumar hana fasa kwauri ta kwastam da ta biya naira miliyan 200 ga wasu mutane 10 da jami’an kwastam suka kashe a garin Jibia na jihar Katsina.
Majalisar ta kuma umarci hukumar kwastam da ta biya naira miliyan 160 ga mutane 8 da aka kashe a jihar Oyo.
Matakin dai ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kwastam na majalisar da ya binciki kashe-kashen al’umma.
A jiya ne dai kwamitin da ke karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar, Idris Wase, ya duba rahoton da shugaban kwamitin kwastam Leke Abejide na jam’iyyar ADC daga jihar Kogi ya gabatar.
A watan Agustan 2021, wata motar kirar Hilux ta Hukumar Kwastam ta yi kan wasu mutane a gefen titi a garin Jibia na jihar Katsina, inda ta kashe mutane da dama.
Wani dan majalisar wakilai, Sada Soli na jam’iyyar APC daga jihar ta Katsina, shine ya gabatar da bukatar a gudanar da bincike kan hatsarin.
A cewarsa wasu jami’an hukumar kwastam sun yi hatsarin ne a yayin da suke bin masu fasa kwaurin shinkafa.