Jiragen yakin sojojin saman Najeriyasun kashe wasu manyan ‘yan ta’addan da sojojinsu a jihar Katsina

0 99

A cigaba da kai farmakin da jiragen yakin sojojin saman Najeriya ke kai wa a yankunan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma, sun kashe wasu manyan ‘yan ta’addan da sojojinsu a jihar Katsina.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa, harin da jiragen yakin sojin saman Najeriya suka kai a garin Ilela da ke jihar Katsina a ranar Lahadin da ta gabata, ya yi sanadiyyar kashe ‘yan ta’adda da dama na sansanonin wasu manyan ‘yan ta’addan biyu mai suna Gwaska Dankarami da Alhaji Abdulkaramu.

An kuma rawaito cewa ‘yan ta’addan da aka kashe su ne suka kai wasu hare-hare a kusa da kananan hukumomin Safana da Dan Musa a jihar Katsina.

An kai harin ne bayan da jiragen yakin sojojin saman Najeriya suka rusa wani kogon dutse da ke wajen garin Ilela, inda ‘yan ta’addan suka saba zuwa su huta da kuma amfani da shi a matsayin mafaka.

Bayan kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Wata majiyar leken asiri ta tabbatar da nasarar harin da aka kai ta sama wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan ta’adda da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: