Shugaban Buhari zai fara ziyarar kwanaki hudu zuwa birnin Addis Ababa daga yau

0 64

Fadar shugaban kasa ta ce a yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fara wata ziyarar kwanaki hudu zuwa birnin Addis Ababa babban birnin a kasar Habasha.

Buhari Zai halarci zaman taron shugabannin kasashen Afirka karo na 35.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

Femi Adesina ya ce shugaba Buhari zai bi sahun sauran shugabannin Afirka wajen nemo hanyoyin magance kalubalen siyasa, tattalin arziki da zamantakewar nahiyar.

Ya ce, Shugaba Buhari zai gana da wasu shugabannin kasashe domin inganta huldar kasuwanci, da hada kai don tinkarar kalubalen tsaro da kuma kulla alaka a bangarori daban-daban domin samun ci gaba mai dorewa.

Femi Adesina ya ce shugaban zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, Ministan Noma, Mohammed Abubakar da Ministan Harkokin Agaji, Kula da Annoba da Walwalar Jama’a, Sadiya Umar Farouk.

Leave a Reply

%d bloggers like this: