An gabatar da kudirin doka da ke neman soke hukumar tsaron fararen hula na civil defense a Majalisar Wakilai

0 130

An gabatar da wani kudirin doka da ke neman soke hukumar tsaron fararen hula civil defense a majalisar wakilai.

Kudirin dokar wanda Shina Peller dan jam’iyyar APC daga jihar Oyo ne ya dauki nauyinsa, na neman a soke dokar hukumar ta civil defense.

Dangane da takaitaccen kudurin dokar, Shina Peller yana bayar da shawarar samar da kwamitin rikon kwarya da zai kula da hukumar, tare samar da ka’idoji da aiwatar da hanyoyin mika kadarori da ma’aikatan hukumar ga rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Shina Peller ya ce ayyukan jami’an tsaron fararen hula civil defense na kamanceceniya da ‘yan sanda. Ya kara da cewa barin hukumar a halin yanzu asara ce.

A mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne aka samar da dokar hukumar tsaron fararen hula civil defense ta shekarar 2003 wacce ta kai ga kafa hukumar.

Kudirin zai bi matakan majalisa kafin a zartar da shi ko kuma a yi watsi da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: