Majalissar masarautar Gumel ta dakatar da wasu hakimai guda biyu da kuma Dagatai hudu bisa laifin samun su da yin sakaci da aiki da kuma nuna halin ko in kula a harkokin tsaro a yankunansu.

Hakiman da aka dakatar sun hadar da na Jeke kuma Kachallan Gumel Alhaji Sani Ibrahim da Hakimin Shabaru kuma Dan Furyan Gumel Alhaji Ismaila Muhammad da kuma Dagatan garuruwan Mai zuwo da Garin Danga da ‘Yan Baro a yankin karamar hukumar Sule-Tankarkar.

Sakataren masarautar Gumel Alhaji Murtala Aliyu ya sanar da hakan bayan kamala taron gaggawa na kwamitin tsaro na masarautar.

Yace taron ya amince da dakatar da hakiman da kuma dagatan har zuwa lokacin da ‘yansanda zasu kamala bincike da kuma gabatar da rahotansu.

Murtala Aliyu ya ce Dagatan da aka dakatar sun kasa gabatar da rahotan matsalar tsaro dake damun yankunansu ga hukumomin tsaro akan lokaci.

Majalisar ta kuma yabawa ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro bisa kama masu garkuwa da mutane.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: