

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu mutane a gidan shugaban kungiyar malaman jami’o’i ASUU na jami’ar tarayya ta Gusau, Abdurahman Adamu.
Haka kuma an yi garkuwa da wani ma’aikacin sashen kudi na jami’ar, Alhaji Abbas, a wani samame da aka kai musu unguwarsu ta rukunin gidajen Damba da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara.
An ginawa ma’aikatan gwamnatin jihar rukunin gidajen ne, amma daga baya aka sayar da su ga daidaikun mutane.
Wani ma’aikacin jami’ar, Anas Sani, ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun zo ne domin shugaban kungiyar ta ASUU.
An rawaito cewa wadanda harin ya rutsa da su sun hada da dan uwa, wa, kane da kuma surukai biyu na Abdurahman Adamu.
Haka kuma an kai hari gidan ma’aikacin sashen kudin, wanda makwabcin shugaban kungiyar ta ASUU ne, amma ba a dauki kowa daga cikin iyalansa ba.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ya ce ba shi da cikakken bayani game da harin.