Wasu dalibai sun maka wata makaranta a kotu bisa haramta musu amfani da hijabi a jihar Oyo

0 91

Wata babbar kotun jihar Oyo da ke Ibadan, karkashin jagorancin Ladiran Akintola, ta sanya ranar 11 ga watan Maris domin cigaba da sauraron karar da ake yi na kare hakkin dan Adam.

Dalibai mata musulmai 11 ne suka gabatar da karar kan makarantar Ibadan International School bisa haramta musu amfani da Hijabi.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya bayar da rahoton cewa, iyayen daliban a madadin ‘ya’yansu sun maka makarantar zuwa kotu saboda tauye hakkin ‘ya’yansu na hana su sanya hijabi a kayan makarantarsu.

A zaman da aka yi a jiya laraba, lauyan wadanda suka shigar da kara, Hassan Fajimite, ya shaida wa kotun cewa ya samu martani daga dukkan wadanda ake kara in banda mutum daya.

Hassan Fajimite ya shaidawa kotun cewa yana bukatar lokaci domin samun martanin wanda ya rage, sannan ya bukaci a dage shari’ar.

Kazalika Lauyan ya bukaci kotun da ta ayyana matakin hukumar makarantar na ci gaba da haramtawa dalibai mata musulmi sanya hijabi a matsayin kuskure, kuma wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: