‘Har yanzu fannin kiwon lafiya a Najeriya na fuskantar wasu manyan matsaloli’ – Osinbajo

0 39

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce har yanzu fannin kiwon lafiyar kasarnan na fuskantar wasu matsaloli masu matukar muhimmanci wadanda suka haifar da mummunan sakamako idan aka kwatanta da tsarin kiwon lafiya a kasashe da suka cigaba a duniya.

Osinbajo ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da kwamitin kawo sauyi a fannin kiwo lafiya a Abuja.

A wata sanarwa da ofishin kula da harkokin gwamnati ya fitar a yau, mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa dole ne a samar da wani shiri na inganta samar da ingantacciyar lafiya cikin sauki ga ‘yan kasa.

A wani labarin kuma, Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bar Abuja da safiyar yau zuwa birnin Accra na kasar Ghana, domin wakiltar Najeriya a wani babban taron koli na kungiyar ECOWAS ta shugabannin kasashen yammacin Afirka da ke tattaunawa kan al’amuran siyasa a Burkina Faso, Mali da Guinea.

Taron wanda ke zuwa a matsayin wani bangare na kudurorin da aka cimma a taron tattaunawa da shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya jagoranta a makon jiya, zai yi nazari ne kan rahoton tawagar ECOWAS da aka aika zuwa Quagadougou domin ganawa da gwamnatin mulkin soja da ta kwace mulki a Burkina Faso kwanannan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: