An gano wani wuri da ake sarrafa gurbataccen man girki a jihar Kano

0 89

Hukumar Kare Hakkin Mai Saye ta Jihar Kano ta ce ta gano wani wuri da ake sarrafa gurbataccen man girki.

Gano man na daga cikin kokarin da hukumar ke yi na kare jama’a daga amfani da kayayyakin da ba su da kyau da na jabu da kuma gurbatattun kayayyaki.

Manajan Daraktan Hukumar, Idris Bello-Danbazau, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai jiya ta hannun mai magana da yawun hukumar, Musbahu Yakasai, a Kano.

Bello-Danbazau, wanda babban mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin tabbatar da inganci, Honorabul Sale Muhammad, ya wakilta ya jagoranci tawagar bincike zuwa wajen da ke Dakata Rinji a karamar hukumar Nasarawa a cikin birnin Kano.

A cewarsa, wajen sarrafa man girkin yana kusa da wata babbar cibiyar tattara shara.

Ya bayyana cewa wajen ba shi da tsafta kuma yana da hadari ga lafiyar jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: