Kungiyar ACRESAL reshen jihar jigawa tace ta horas da manyan manoma 120

0 197

Kungiyar ACRESAL reshen jihar jigawa tace ta horas da manyan manoma 120 dabarun ayyuka da bunkasa samar da abinci a masarautun Ringim, Hadejia da Gumel.

Kodinaton ayyuka na kungiyar Alhaji Yahaya Muhammad Kafin Gana ya bayyana haka yayin shirin horaswar daya gudana a cibiyar koyar da sana’oin dogaro da kai ta Hadejia.

Yace horon zai bawa mahalarta taron damar koyon dabarun ingantawa da iri.

Kodinatan ya shawarci mahalarta taron da suyi amfani da ilimin da suka koya domin bunkasa harkokin samar da abinci a jiha da kuma bunkasa tattalain arziki da walwalarsu.

Alhaji Yahaya Muhammad Kafin Gana ya godewa masu horarar war bisa kyakkyawan aiki da suka yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: