A jawabinsa shugaban kwamitin zakka na masarautar Barista Abdulfatah Abdulwahab ya bukaci masu hali a cikin alumma dasu rinka bada zakka domin tsarkake dukiyoyinsu
Shugaban wanda ya samu wakilcin babban limamin Hadejia Mallam Yusif Abdulrahman Ya’u yace ana raba zakka a inda aka tara ta dan haka ya shawarci wadanda suka sami zakkar dasu yi amfani da ita ta hanyar data dace
Rabon da aka yi a gonar Adamu Maje dake garin Hadejia, a yayin jawabinsa sakataren kwamitin Injiniya Ismaila Garba Barde yace an raba zakkar shinkafa da masara da Dawa da aka bayar a matsayin zakka a gonar ga mabukata.
A jawabinsa daya daga cikin wadanda suka sami zakkar Malam Ibrahim Usman ya yaba da kokarin kwamitin na karba da kuma rabon zakka na masarautar.