Kungiyar Makarantu masu zaman kansu na jihar Kano ta yi barazanar yin fito-na-fito da gwamnatin jihar

0 293

Kwamitin hadin gwiwa na kungiyar Makarantu masu zaman kansu, gamayyar duk wasu makarantu masu zaman kansu a jihar Kano, ta yi barazanar yin fito-na-fito da gwamnatin jihar yayin da aka koma makarantu a yau.

Gidan rediyon Sawaba ya ruwaito cewa, mai ba gwamnan jihar shawara na musamman kan makarantu masu zaman kansu, Alhaji Baba Umar Abubakar, a watan Yuli ya sanar da soke lasisin gudanar da dukkan makarantu masu zaman kansu a jihar tare da umartas su da su sabunta ta kafin su koma aiki a watan Satumba.

Da yake jawabi ga manema labarai jiya a Kano a madadin masu makarantun, daya daga cikin wadanda suka shirya taron, Engr. Bashir Adamu Aliyu, ya bukaci masu makarantun su koma aiki a yau Litinin kamar yadda suka tsara. Sai dai Bashir Adamu ya yi kira ga kafafen yada labarai da sauran jama’a da su sanya ido kan duk wani abu da zai faru yayin da aka koma makarantu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: