Shugaba Tinubu ya amince da kudi naira biliyan 50 domin taimakawa jihohin arewa maso yamma

0 196

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa shugaban kasa bola Tinubu ya amince da kudi naira biliyan 50 domin taimakawa jihohin arewa maso yamma da ayyukan ta’addanci yayi kamari domin bunkasa harkokin gine-gine.

Shattima ya bayyana haka ne yayin da yai ziyarar ta’aziyya ga mai martaba sarkin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad-Mera a fadar sa dake Argungu bisa rasuwar shehin malamin Islama Abubakar Giro wanda ya rasu a ranar larabar makon jiya.

Yayi bayanin cewa shugaban kasa Bola Tinubu yana kyakkyawar aniyar tallafawa al’umar arewacin Najeriya musamman yankunan da rikicin ta’addanci da ayyukan masu garkuwa da mutane da dai-daita.

Shattima ya bayyana jihohin da zasu ci gajiyar kudaden da suka hada Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina da kuma jihar Kaduna, ya kuma ce jihohin Neja da Benuwai suma zasu amfana da tallafin.

Kazalika a cewarsa jihohin Jigawa da Kano kai tsaye ib’tilain rashin tsaaron bai shafe su ba kamar sauran.

Haka kuma ya sake tabbatar da kudurin gwamnati na gina gidage 1000 a duka fadin jihohin da rikice-rikicen ya shafa nan da dan wani lokaci, inda yace shirin zai fara ne kodai daga jihar Sokoto ko kuma Jihar Kebbi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: