Gwamnatin shugaba Tinubu zata magance kalubalan da fannin kiwon lafiya ke fuskanta

0 253

Ministan Lafiya da walwalar jama’a Farfesa Muhammad Ali Pate, yace gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu zata magance kalubalan da fannin kiwon lafiya ke fuskanta a kasar nan.

Muhammad Fate ya fadi haka ne a jiya, yayin bude taron kimiyya dana kungiyar likitoci da likitocin hakora ta Najeriya karo na 13, a Kano.

Ministan wanda ya samu wakilcin shugaban Asibitin koyawar na Aminu Farfesa Abdulrahman Sheshe, yace kalubalai masu tarin yawa da fannin kiwon lafiya ke fama da su a kasar nan.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya zata aiki kafada-da-kafada da kungiyoyin likotoci domin domin cimma burin habaka fannin lafiya a Najeriya.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar likitoci ta kasa, Dakta Victor Makanjuola, ya koka da yadda kwararrun likitocin ke ficewa daga kasar domin neman wuraren kiwo.Shima kwaminan lafiya na jihar Kano Dakta Yufus Labaran ya yabawa kungiyar likitocin wajen gudanar da shirin na wannan shekara a jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: