Badaru ya bukaci yan Najeriya su cigaba da addu’a domin kawo karkashen matsalar tsaro a kasar nan

0 255

Ministan tsaro Muhammadu Badaru Abubakar, ya bukaci yan Najeriya sun cigaba da addu’a domin kawo karkashen matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.

Muhamamd Badaru yayi wannan kira ne a jiya yayinda ya karbi bakuncin tawagar gwamnan Jihar Jihawa Malam Umar.

Ministan tsaron yace matsalar tsaro da sauran abubuwan cigaban kasa suna bukatar addu’a kafin a samu nasara a kan su.

Da yake jawabi kan fatan da yake dashi na magance matsalar tsaron, tsohon gwamnan jihar jigawan ya nemi hadin da addu’ar yan Kasa, domin a samu zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.

Tunda farko, Gwamnan Jihar Jigawa wanda ya jagoranci shugabannin addini dana gargajiya, da yan kasuwa da sauran masu rike daga ofisoshin gwamnati daga jihar Jigawa,yace manufar wannan ziyara shine taya Ministan murnar da kuma tabbatar masa bashi hadin kai a kowanne lokaci. Gwamnan ya kuma tunasar da Ministan cewa yan Najeriya sun da kyakkyautan zaton cewa zai bada fifiko a fannin tsaron kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: