Kungiyar gwamnonin Najeriya ta jaddada kin amincewa da karin mafi karancin albashin ma’aikata

0 123

Yayin da gwamnatin tarayyar Najeriya ke cigaba da tayin mafi karancin albashi na N62,000 a duk wata, gwamnonin jihohi karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya sun jaddada kin amincewarsu kan karin mafi karancin albashin ma’aikata.

Wata majiya ta bayyana cewa matsayin gwamnonin a taron kwamitin mafi karancin albashi da aka gudanar na ranar Juma’a, ta ce gwamnonin sun yi imanin cewa duk wani kudirin biyan albashi na tilas a jihohin zai iya haifar da sallamar kusan kashi 40 na ma’aikata a jihohin.

Majiyar ta kara da cewa galibin jihohin na fama da dimbin basussuka, saboda basussukan da magabatansu suka karba, saboda haka ba za su iya biyan sabon mafi karancin albashi ba, ta kuma kara da cewa jihohi 10 ne kawai za su iya biyan sabon mafi karancin albashi.

Jihohi 10 da za su iya biyan sabon mafi karancin albashin sun hada da jihar Legas, Delta, Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Ribas, Ogun, Kano, da Kaduna.

Gwamnonin sun bayyana a taron na ranar Juma’a cewa mafi karancin albashi na N60,000 ba abu ne mai dorewa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: