Hukumar NUPRC ta sanar da cewa ta na shirin samar da iskar gas kaso 50 cikin 100 a kasar nan

0 155

Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta kasa NUPRC a jiya, ta sanar da cewa ta na shirin samar da iskar gas mai kaso 50 cikin 100 a kasar nan ta hanyar shirin kasuwanci na samar da iskar gas na kasa (NGFCP).

Da yake jawabi a lokacin da shugabannin kungiyar bunkasa muhalli ta HEDA suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja, shugaban hukumar Gbenga Komolafe, ya bayyana cewa, Nijeriya ta riga ta cimma burin rage fitar da iskar methane da kashi 60 cikin 100 daga man fetur da iskar gas.

Ya bayyana cewa, Hukumar ta yi aiki tare da hukumomin tsaro da sauran hukumomin gwamnati don dakile matsalar satar man fetur kuma tuni kokarin ya samu sakamako mai kyau.

Komolafe ya ce kar kashe kudaden da kamfanonin mai na kasa da kasa (IOCs) suka yi a baya-bayan nan, ko shakka babu ya haifar da damuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: