Kungiyar kiristoci ta ce illar tabarbarewar tattalin arziki ba abu ne da talakawa zasu iya jurewa ba

0 189

Kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ta ce illar tabarbarewar tattalin arziki da ake fama da ita a kasar na zama abin da ba zai iya jurewa ga talakawan Najeriya ba.

Kungiyar a jihohin Arewa 19 da Abuja ta bayyana hakan a ranar Juma’a.

Kungiyar ta yi nuni da cewa kalubalen tsaro da ke kara ta’azzara ya zama abin damuwa matuka.

Kungiyar CAN ta Arewa a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun babban sakatarenta, Elder Sunday Oibe, a Kaduna, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakin magance tabarbarewar tattalin arziki da tabarbarewar tsaro a kasar nan.

A cewar sakatariyar kungiyar, wahalhalun da ake fama da su a kasar na kara zama kasala ga talakawan Najeriya saboda tsadar kayan masarufi, sufuri, kayayyaki, da kuma ayyuka sun sanya ‘yan Najeriya da dama cikin mawuyacin hali.

Ya kara da cewa, duk wadannan suna da nasaba da karuwar rashin tsaro da ake samu ta hanyar kashe-kashe da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa. Ya kuma ce kungiyar kiristocin ta yi bakin ciki kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare a jihar Filato, inda aka kashe mutane akalla 300, yayin da ya yi kira ga gwamnati da ta yi duk mai yiwuwa don dakile kashe-kashen ba a Filato kadai ba har ma a fadin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: