Kungiyar manyan likitocin dabbobi tayi Allah wadai da kashe wasu kananan giwaye da aka yi a Borno

0 273

Kungiyar manyan likitocin dabbobi ta kasa tayi Allah wadai da kashe wasu kananan giwaye da aka yi a karamar hukumar Kala Balge dake jihar Borno.

Haka nan kungiyar ta nuna damuwa kan yadda aka kashe wasu shaho guda biyu a yankin jihohin Kebbi da Sakwwato wadanda suka yi hijira daga yankin Turai.

Shugaban kungiyar na kasa Dr. Moses Akoroyo, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Yace abin takaici ne yadda aka nuna wani faifan bidiyo a shafin sada zumunta na yadda wasu jami’an soji suka hallaka wasu giwaye.

Moses, ya kara da cewa kungiyar tana sanar da sauran abokan aikinta da hukumomin kula da Gandun daji cewa suna sane da wannan labarin. Kazalika shugaban kungiyar yace za su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile wannan al’amari na kashe dabbobin daji dake neman zama ruwan dare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: