Hukumar NDLEA ta kama miyagun kwayoyi masu nauyin kilogram 100,458

0 151

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kaduna, ta kama miyagun kwayoyi masu nauyin kilogram dubu 1 dari 458 a cikin watan Disamba.

Wannan dai na kunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Talata dauke da sa hannun jami’in yada labarai na hukumar Sha’aibu Omale.

Omale, yace abubuwan da hukumar ta kama sun hada da kwayoyin tiramadol da koken da sauran miyagun kwayoyi. Hakalika mai magana da yawun hukumar yace an damke wasu mutane 103 da ake zargi da alaka da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: