Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya  da na wadanda ba malamai ba sun fara yajin aiki

0 119

Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya  da na wadanda ba malamai ba sun fara yajin aikin a fadin kasar nan sakamakon abin da suka bayyana a matsayin rashin adalci da kuma banbance-banbance na biyan albashin da gwamnatin tarayya ke yi.

Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in ta kasa Mohammed Ibrahim, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau.

Ya koka da cewa babu wani wakilin gwamnati da ya tuntubi kungiyoyin wanda yace hakan sam ba adalci bane ga kungiyoyin. Shugaban kungiyar ya ce Ministan Kwadago Nkiruka Onyejeocha bai tuntubi kungiyoyin ba duk da cewa an bayar da sanarwar kwana bakwai a ranar Litinin din da ta gabata, wani mataki da suka ce anbi sak irin salon  tsohon Ministan Kwadago Chris Ngige.

Leave a Reply

%d bloggers like this: