Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaga da Magumeri da Gubio a majalisar wakilai ya raba kayan abinci ga iyalai 5,000

0 192

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaga da Magumeri da Gubio a majalisar wakilai ta kasa Usman Zannah, ya raba kayan abinci ga iyalai 5,000 domin rage wahalhalun da ake fuskanta a mazabarsa da jihar Borno.

Yan kungiyar sa kai, mafarauta, da da ’yan banga da ke yaki da ta’addancin Boko Haram, kungiyoyin matasa da mata ne suka ci gajiyar tallafin na Ramadan.

Ya godewa shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum bisa dukkan goyon bayan da suka bayar wajen ganin an kwato yankunan mazabarsa da ke fama da rikici.

Hakama Sanata Sunday Katung  na jam’iyyar PDP mai wakiltar Kaduna ta Kudu ya raba tirela dauke da buhunan shinkafa ga marasa galihu dake yankin sa. Shugaban kwamitin rabon kayayyakin abincin, Danlami Shuaibu Zango ya ce tallafin abincin na daga cikin kokarin da Sanatan ya yi na taimakon al’umma a cikin wata mai alfarma domin rage radadin matsin tattalin arziki musamman ma ga marasa galihu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: