Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 14 a kauyen Dogon Noma-Ungwan Gamo

0 136

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 14 a kauyen Dogon Noma-Ungwan Gamo da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Lamarin ya zo ne mako guda bayan da aka yi garkuwa da mutane 61 a kauyen Buda da ke karamar hukumar Kajurun.

Hukumomin ‘yan sanda ba su tabbatar da harin ba.

Sai dai wani shugaban matasa Sani Musa ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne a safiyar ranar Asabar din da ta gabata a yankin Dogon Noma.

Yace yan bindigar sun kuma  yi ta harbin sama, inda daga bisani suka yi awon gaba da mutane goma sha hudu yayin da mutum daya ya samu rauni. A cewar shugaban matasan, wanda ya samu rauni daya tilo, Jibrin Dauda, ​​an kai shi asibiti domin kula da lafiyarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: