Sanata Abdul’Aziz Yari ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin Ramadan wajen yi wa Shugaba Bola Tinubu addu’a

0 226

Sanata Abdul’Aziz Yari jam’iyyar APC daga jihar Zamfara, ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin Ramadan wajen yi wa Shugaba Bola Tinubu addu’a, domin daidaita tsaro da tattalin arzikin kasa.

Shugaban kwamitin yada labarai na wata kungiyar siyasa ta Yari Ibrahim Muhammad ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar jiya a Gusau.

Sanata Abdul’Aziz Yari, wanda tsohon gwamnan Zamfara ne, a halin yanzu yana wakiltar mazabar Zamfara ta yamma a majalisar dokokin kasa.

Sanatan ya ce al’ummar kasa da shugabanninta na bukatar addu’a daga kowa da kowa. Yari kuma ya bayar da gudummawar Naira 50,000 ga mutume 2,500 da za su halarci wani shirin tallafi na Ramadan na kwanaki biyar da kuma tufafi kala daya gabanin bikin Sallah.

Leave a Reply

%d bloggers like this: