Kungiyar NAWOJ ta nemi a samar da dokar da zata kara bayar da kariya, yanci da kuma damarmaki ga mata

0 125

Kungiyar mata yan jarida ta kasa reshen jihar Jigawa, tayi kira da a samar da dokar da zata kara bayar da kariya, yanci da kuma damarmaki ga mata da kuma sassauta dabai-bayin da al’adu suka yi musu.

Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da shugabar kungiyar Hauwa Ibrahim Ladan ta sanya wa hannu ta kuma rabawa manema labarai.

Kungiyar ta kuma yi kira da a shigar da mata cikin harkokin gudanar da gwamnati da kuma basu dama wajen damawa dasu a kowanne bangare a cikin al’umma. Ta kara da cewa idan aka sanya irin wadannan dokoki aka kuma sahale, tare da bayar da goyon baya ga mata a fannin kasuwanci, aikin hannu da kananan sana’o’I zai inganta cigaban zamantakewa, da kuma cigaban walwala da nasarar kowacce mace a cikin al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: