Dakarun tsaro sun yi nasarar kashe yan awaren IPOB/ESN guda 20

0 76

Dakarun tsaro sun yi nasarar kashe yan awaren IPOB/ESN 20 yayin wani samame da suka kaddamar a yankin karamar hakumar Orsu dake jihar Imo.

Samamen wanda aka gudanar a ranar 7 ga watan Maris, wandanda dakarun Udo Ka, da yan sanda, jami’an tsaron farin kaya DSS, da jami’an tsaron farar hula sibil defens suks gudanar.

Da yake tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, daraktan yada labarai na tsaro Major Janar Edward Buba, yace dakarun sun tarwatsa mobayar batagarin na IPOB ciki harda Babbar hedikwatar su, da kuma kananan tashohi, dakin iko tare da dukkan guraren buyan su.

Dakarun sun kuma tarwatsa maboya da ofishin yan awaren Buteuzor, tare da kwato kayayyakin laifi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: