An dage haramcin sayar da ci da sayar nama a Kampala babban birnin kasar Uganda

0 123

Hakumomi a Uganda sun dage haramcin sayar da ci da sayar nama a Kampala babban Birnin kasa, duk da barkewar wata cuta da ke kama kofato da kuma bakin dabbobi.

Hakumomin lafiya a kasar cikin makon daya gabata sun sanya dokar haramci tare da rufe duk kasuwannin sayar da nama da mayanku domin takaita yaduwar cutar a cikin jama’a.

Amma Ministan babban Birnin na Kampala Minsa Kabanda ya sanarwa jaridar Daily Monitor cewa gwamnati ta dage dokar, yayin da ta samu cigaba a aikin lalubo bakin zaren cutar a babban Birnin kasar.

Minsa Kabanda ya kuma roki jama’a da su tabbatar da yin gwaji ga dabobi gabanin yanka su.

Yan kasuwa a Birnin dai da dama basu goyi bayan matakin ba, suna masu sukar gwamnati da yunkurin fakewa da kafa wata kafa wajen takurawa jama’a. Bayanai sun ce cutar da aka gano mai kama kofato da bakin dabbobi ta bulla a unguwanni 40 na Birnin kamar yadda kafofin yada labarai na cikin gida suka rawaaito.

Leave a Reply

%d bloggers like this: