Kungiyar NULGE ta Jihar Jigawa ta raba kayan tallafi ga mambobin kungiyar marasa karfi

0 110

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa NULGE rashen karamar hukumar Birniwa ta yabawa uwar kungiyar ta Jiha bisa raba kayan tallafi ga mambobin kungiyar marasa karfi.

Shugaban kungiyar na karamar hukumar Comrade Garba Rabiu Hamza shine yayi wannan yabo, yayin kaddamar da rabon kayan tallafin ga ma’aikatar karamar hukumar.

Comrade Garba Rabiu Hamza yace rashen kungiyar na karamar hukumar ya karbi tallafin buhunan shinkafa 50 daga uwar kungiyar ta Jiha. Sanann ya yabawa kwamishinan kananan hukumomi Hon Muhamned Garba MK bisa amincewa da siyan kayan tallafi domin rabawa a kananan hukumomi 27 na jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: