Za’a dakatar da sahihancin takardun digirin Uganda, Kenya da kuma jamhuriyar Nijar

0 172

Biyo bayan dakatar da sahihancin takardun digiri na kasashen jamhuriyar Benin da Togo, gwamnatin tarayya tace zata fadada dakatarwar zuwa wasu kashe ciki hadda Uganda, Kenya da kuma jamhuriyar Nijar.

Ministan Ilimi na kasa Tahir Mamman shine ya sanar da haka yayin tattaunawarsa da gidan Talabijin na Canals.

Tunda farko dai gwamnatin tarayya ta soke sahihancin takardun digiri na wasu kasashen yammacin Afrika masu amfani da harshen Faransanci, biyo bayan wani bincike da aka gudanar. Ya kara da cewa hukumomin tsaro zasu bangado masu amfani da takardun bogi na wasu jami’o’in kasashen waje domin neman damar-maki a kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: