Ba’a samu nasara ba a tattaunar mu da gwamnatin tarayya kan batun mafi karancin albashi

0 225

Kungiyar Kwadago ta masu masana’antu TUC, ta bukaci gwamnatin tarayya ta yi amfani da yarjeniyoyin da suka cimma a shekarar da kungiyoyin kwadago a shekarar 2023, musamman batun mafi karancin albashi.

Shugaban kungiyar na TUC Festus Osifo da sakataran kungiyar Malam Nuhu Toro, sune suka bayyana haka cikin sakon sabuwar shekarar da suka fitar.

Mista Osifo yace kungiyar ta TUC tayi kokarin ganin sun tattauna tsakanin su da gwamnatin tarayya, amma sai dai ba’a samu nasara a tattaunar su da gwamnati ba.

Mista Osifo, yace ya kamata a yi amfani da tsarin mafi biyan karancin albashi, da kuma biyan bashin albashin da ma’aikata ke bi. Shugaban kungiyar ya bukaci gwamnatin tarayya data Jiha da su dauki dukkan matakai na magance matsalar tattalin arziki da dena ciyo bashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: