Sanata Barau Jibrin ya raba tallafin motocin sufuri 60 a mazabar da yake wakilta a Kano

0 170

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya raba tallafin motocin sufuri 60 a mazabar da yake wakilta a Kano.

Cikin wata sanarwa da hadimin sa a kafafan yada labarai Ismail Mudashir ya fitar, yace dukkan mazauna jihar zasu amfana da motocin, ciki hadda ‘Yan kasuwa, Manoma, ma’aikatan gwamnati, ‘Yan siyasa da sauran su.

Da yake jawabi yayin kaddamar da bada motocin, yace an samar da motocin ne domin saukakawa matafiya zuwa wuraran aiki, kasuwa da gona domin habaka tattalin arziki a Jihar.

Mataimakin shugaban majalisar ya jaddada kudirin sa na cigaba da taimakawa mazabar sa domin inganta tattalin arziki ta hanyar samarwa mutane abubuwan dogaro da kai. Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi da su yi amfani da ababan hawan yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: