Kungiyar Yan Bulala ta Jihar Jigawa ta amince da kafa kwamiti mai wakilai tara

0 272

Kungiyar Yan Bulala ta Jihar Jigawa ta amince da kafa kwamiti mai wakilai tara, karkashin amincewar uban kungiyar Umar Kabiru Dubantu

Wakilan kwamitin sun hadar da Alhaji Ibrahim Korsa a matsayin shugaba da Damina Bashsha mataimakin shugaba da Alasan Gagarawa sakatare da Lamido Wada Kwamandan kungiya na jiha da sauran shugabannin kungiyar

A wata sanarwa da kungiyar ta aiko dakinmu na labarai tace an kafa kwamitin ne domin sake inganta aiyukan kungiyar a fadin jihar nan Kungiyar ta nemi Karin hadin kai da goyan bayan alumma wajen marawa kudirin jamian tsaro baya na inganta harkokin tsaro a fadin jihar nan

Leave a Reply

%d bloggers like this: