Matashi dan bautar kasa NYSC da aka yi garkuwa dashi ya shaki iskar ‘yanci

0 268

Babban daraktan hakumar hidimtawa kasa ta matasa NYSC Brigadier General Yushau Ahmed yace daya daga cikin matasa masu hidima wa kasa, da aka yi garkuwa da shi yayin da yake kan hanyar sa ta Uyo a Akwa Ibom zuwa Sokoto ya shaki iskar yanci yayin da har yanzu 7 ke hannun yan bindiga.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan babban taron masu ruwa da tsaki ji a Abuja, daraktan yace anyi garkuwa dasu ne cikin dare.

A wani labarin kuma, Kungiyar ‘yan Jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Zamfara ta nuna alhininta kan mutuwar Hamisu Danjibga da ya kwashe shekaru yana aikin jarida a ƙasar.

An tsinci gawar ɗan jaridar – wanda ke aiki da kafar yaɗa labarai ta VON – cikin wani rami da ke bayan gidansa kwana uku bayan ɓacewarsa.

Wasu ɗaliban makarantar islamiyya ne suka gano gawarsa ranar Laraba da maraice cikin wani rami da ke bayan gidansa, inda suka yi gaggawar ankarar da malamansu.

Kungiyar NUJ reshen jihar cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana takaicinta kan halin da ɗan jaridar ya mutu. Ta kuma yi kira ga jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin tare da hukunta su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: