Kwamatin Majalisar Dattawa ya bayar da shawarar rage wa ‘yan majalisa albashi

0 134

Kwamatin Majalisar Dattawa da ke nazari kan dokar zabe, ya bayar da shawarar rage wa ‘yan majalisa albashi da kuma masu mukaman gwamnati.

Shugaban kwamatin, Sanata Sharafadeen Ali ne, ya bayyana hakan a jiya Litinin.

Ya bayyana hakan ne, yayin da gana da ‘yan siyasa da kuma wakilai a bangaren shari’a game da aikin kwamitinsa na yi wa dokar zabe ta 2022 kwaskwarima.

Ya ce suna bayar da shawarar rage albashin ‘yan majalisar da kashi 30 cikin 100, yayin da za a rage na masu rike da mukamai da kashi 40 domin rage kashe kudin gwamnati.

Jam’iyyun sun kuma nemi a hada katin zabe da lambar dan kasa ta NIN domin kara tsaro da kuma rage kashe kudi wajen yin rajistar katin zabe.

A baya-bayan nan dai gwamnatin tarayya ta kara wa’adin hada layukan waya da lambar NIN zuwa karshen watan Satumba. 

Leave a Reply

%d bloggers like this: