Kwamittin rabon arzikin kasa ya raba kudi ₦907,054,000,000 a watan Yuni

0 397

Kwamittin rabon arzikin kasa ya raba kudi naira bilyan dari tara da bakwai da naira milyan hamsin da hudu ga gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi a watan Yuni 2023.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwar bayan taron kwamittin wanda ya gudana a watan Yuli da muke ciki, kamar yadda daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ofishin akanta janar na kasa Bawa Mokwo ya fitar a Abuja.

Dr. Oluwatoyin Madein, babban akanta janar na kasa shi ne ya jagoranci taron.

Sanarwar tace daga cikin jumullar kudaden shiga naira bilyan dari tara da bakwai da naira milyan hamsin da hudu da aka raba, gwamnatin tarayya ta karbi naira bilyan dari uku da arba’in da biyar da mliyan dari biyar da sittin da hudu.

Sai kuma gwamnatocin jihohi da suka karbi naira bilyan dari biyu da casa’in da biyar da naira milyan dari tara da arba’in da takwas. Kanana hukumomi  kuma sun samu jumullar kudi naira bilyan dari biyu da sha takwas da naira milyan sittin da hudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: