Majalisar Ɗinkin Duniya ta saka Isra’ila da Hamas cikin jerin kasashe masu cin zarafin Ƙananan yara

0 242

A karon farko, Majalisar Ɗinkin Duniya ta saka Isra’ila da Hamas cikin jerin kasashen da suka aikata abun da ta kira abun kunyar cin zarafin Ƙananan yara.

A cikin rahotonsa na shekeara-shekara kan yadda tashe-tashen hankali ke shafar yara, Sakatare Janar, na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce yaƙin da ake yi a Gaza ya haifar da cin zarafin yara da ba a taɓa ganin irinsa ba.

Gwamnatin Isra’ila ta mayar da martani a fusace bayan ɓullar labarin shirin ɗaukar wannan mataki a makon jiya.

Firaministan ƙasar, Benjamin Netanyahu, ya bayyana matakin na Majalisar Ɗinkin Duniya a matsayin wasan kwaikwayo.

Ita dai Majalisar Ɗinkin Duniya na sakin sunayen ne domin kunyata duk ƙasar da aka samu da laifi irin wannan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: