Jahar Jigawa ta rabawa wa matasa 300 baburan hawa da akwatina da magunguna don yin rigakafin Dabbobi

0 134

A yunƙurinta na inganta lafiyar dabbobi a jahar Jigawa, gwamnatin jahar ta rabawa wa matasa 300 baburan hawa da akwatinan magungunan rigakafin dabbobi da zasuyi aiki a faɗin mazaɓu 287 domin yin rigakafin cututtukan dabbobi.

Gwamnatin jahar Jigawan dai ta ɗauki waɗannan matasan ne waɗanda keda shedar karatu kan ilimin kiwon lafiyar dabbobi ta kuma basu horo na musamman domin gudanar da wannan aiki, ana saran zasu shiga lungu da saƙon jahar Jigawa su gudanar da aikin tabbatar da lafiyar dabbobi.

Yayin ƙaddamar da wannan shiri a ranar Laraba a sansanin ƴan yiwa ƙasa hidima dake Fanisau Dutse, kwamishinan aikin gona na jahar Jigawa Alh. Muttaka Namadi, yace an bullo da wannan shiri ne da nufin bunƙasa kiwo da inganta lafiyar dabbobi a jahar Jigawa, yana mai bayyana cewar hakan bawai kaɗai zai inganta lafiyar dabbobi bane a jahar ta Jigawa harda mutanen jahar kasancewar wasu cututtukan da mutane ke kamuwa dasu daga dabbobi ne.

A jawabinta wakiliya daga majalisar likitocin dabbobi ta ƙasa Dr. Helin ta yabawa gwamnatin jahar Jigawa bisa ɓullo da wannan tsari, inda tace hakan yayi daidai da yunƙurin da majalisar ta likitocin dabbobi ta ƙasa keyi wajen ganin kowace jiha a ƙasarnan ta rungumi wannan shiri, ta kuma bayyana jahar Jigawa amatsayin jahar data fara aiwatar da wannan shiri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: