Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da buƙatar shugaban ƙasar Tinubu ya karɓo rancen $800M

0 252

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da buƙatar shugaban ƙasar Bola Tinubu ya karɓo rancen dala miliyan 800 don gudanar da shirin samar da tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.

Haka kuma Majalaisar ta yi gyara fuska ga dokar ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2022.

Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Godswill Akpabio ne ya karanto buƙatar shugaban ƙasar cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisar.

Tinubu ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasar Muhammdu Buhari ta amince da karɓo ƙarin rancen na dala miliyan 800 daga Bankin Duniya, domin aiwatar da shirin tallafin.

Shugaban ya ce maƙasudin shirin, shi ne domin taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi don su samu abin biyan buƙataunsu na rayuwa.

A jiya Alhamis ma Shugaba Tinubu ya bayyana shirin gwamnatinsa na bai wa gidajen talakawan ƙasar nan miliyan 12 Naira dubu 8,000 na tsawon watanni shida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: