Majalisar dattijai tayi watsi da kudirin siyan sabbin jiragen shugaban ƙasa da na mataimakinsa

0 117

Shugaban majalisa0r dattijan Najeriya, Godswill Akpabio ya bayyana cewa majalisar ba ta amince da a sayi sabbin jiragen shugaban ƙasar da na mataimakinsa ba.

Akpabio ya yi watsi da wani rahoto da ke nuna cewa majalisar dattawan za ta amince da sayen sabbin jiragen sama ga Bola Tinubu da Kashim Shettima duk da ƙalubalen tattalin arzikin da Najeriya ke fama da shi.

Wannan rahoto ya biyo bayan shawarar da kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro ya bayar na sayen sabbin jiragen sama saboda matsalolin da jiragen shugaban ƙasar ke fuskanta.

A kwanakin baya ne shugaba Tinubu ya yi amfani da jirgin sama na ƴan kasuwa domin halartar bikin rantsar da shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afrika ta Kudu.

Fadar shugaban ƙasar ta kare buƙatar samar da sabbin jiragen sama ga shugaban da mataimakinsa yayin da take mayar da martani ga sukar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi ya yi, wanda ya kira shirin da rashin hankali.

BAS

Leave a Reply

%d bloggers like this: