Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta amince da ƙarawa Jami’an ƴansanda albashi da kaso 20 cikin 100

0 223

Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da karawa Jami’an yan sanda Albashi da kaso 20 cikin 100.

Ministan Ma’aikatar Yan sanda Maigari Dingyadi, shine ya bayyana hakan a yau, bayan kammala zaman Majalisar zartarwa wanda shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, a fadar sa dake Abuja.

Ministan ya ce ana saran sabon karin Albashin zai fara aiki daga watan Janeru na shekarar 2022.

Haka kuma ya ce karin albashin ya kunshi kudaden su na Alawus-Alawus da kaso 6, inda kuma aka ware Naira Biliyan 1 da MIliyan 12 domin biyan hakkokin da yan sandan suke bin gwamnati daga shekarar 2013 zuwa 2020.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi alawarin karawa yan sanda albashi domin tabbatar da cewa sun samar da tsaro a kasa.

Kazalika, Majalisar Zartarwar ta amince da kashe Naira Biliyan 13 da Miliyan 100 domin biyan hakkokin yan sanda dubu 5,472 wanda suka mutu a lokacin da suke bakin aiki daga shekarar 2013 zuwa 2020.

Leave a Reply

%d bloggers like this: