Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP ya rasu

0 97

Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Sanata Babayo Garba Gamawa ya rasu.Ya rasu ne ranar Juma’a a Bauchi bayan wata gajeruwar rashin lafiya.

Mai magana da yawunsa, Garba Gadau ya tabbatar da mutuwar ga wakilin jaridar Daily Trust ta waya.“Ya ce yana fama da ciwon ciki kaɗan, aka kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa, ATBU, inda aka kwantar da shi.

Ina kan hanyar zuwa gidansa yanzu”, in ji mai magana da yawunsa.Mista Gamawa, tsohon ɗan Majalisar Jiha, wanda ya taɓa zama Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi a wani lokaci ya canza sheƙa zuwa jam’iyyar APC kafin zaɓen shekara ta 2019, bayan jam’iyyar hamayya ta PDP ta dakatar da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: