Matar shugaba Buhari ta yi kira ga hukumomin da su tabbatar da adalci ga Hanifa Abubakar wacce aka kashe ta a Kano

0 100

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da adalci ga Hanifa Abubakar, yarinya ‘yar shekara biyar da malaminta Abdulmalik Tanko ya yi garkuwa da ita tare da kashe ta.

Aisha Buhari ta yi wannan kiran ne a gidan gwamnatin Kano a jiya a lokacin da ta ziyarci jihar domin ta’aziyyar rasuwar Hanifa da Sheikh Ahmad Bamba.

Uwargidan shugaban kasar ta samu tarba daga Gwamna Abdullahi Ganduje da mai dakinsa Hafsat Ganduje.

A jawabin da ta yi a gidan gwamnati, Aisha Buhari ta ce ta je Kano ne domin ta’aziyya ga gwamnatin jihar da iyalai da al’ummar jihar bisa rasuwar Sheikh Ahmad Bamba da kuma jajantawa iyayen Hanifa kan kisan gillar da aka yi mata.

Ta koka da yadda malamin Hanifa ya ci amanar iyayenta.

Ta jajantawa al’ummar jihar Kano bisa wannan mummunan lamari kuma ta jajantawa gwamnati da iyalan marigayi Sheikh Ahmad Bamba bisa rasuwarsa.

Daga nan sai uwargidan shugaban kasar ta roki Allah Madaukakin Sarki da ya jikan su ya kuma baiwa iyalansu hakurin jure rashin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: