Rundunar yansanda jihar jigawa na sanar da alumar jihar jigawa, musamman wadanda suka nemi shiga aikin dan sandan a shekarar 2021 a matsayin kurata, wadanda ba’a tantance ba, dasu hallara tare da takardun su gobe juma’a 11 ga watan fabareru, a hedkwatar Hakumar yan sanda ta jihar Jigawa da ke dutse babban birnin jiha, da misalign karfe 8 na safe, Domin a tantance su.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin kakakin rundunar yan sandan jihar ASP Lawan Shiisu Adam, ta cikin wani sakon murya da ya aikewa gidan radio sawaba, da safiyar yau.

A cikin Sanarwar ta dakiku 36, Kakakin yace bata shafi wadanda aka tantance tun da fari ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: