Matasa 16,000 ne suka nemi aikin dan sanda a jihar jigawa

0 173

Akalla matasa dubu 16 ne suka nemi aikin dan sanda a matakin kurata cikin gurabe 270 da jihar jigawa ke da shi.

Kakakin hakumar yan sanda na jihar Jigawa DSP Lawan Shiisu Adamu, ya bayyana haka ga manema labarai.

A cewar sa kwamashinan yan sanda na jihar A.T. Abdullahi ya jaddada cewa, daukar aikin kyauta kuma ba’a bukatar komai a hannun masu neman shiga aikin.

Ya bayar da tabbacin cewa za’a tabbatar da daukar wadanda suka cancanta bisa kwazo cikin adalci.

Ya shawarci matasan dasu kiyayi fadawa komar yan damfara, da zasu iya amfani da wannan dama kan wadanda basu jib a basu gani ba. An tsara tantance matasan kuratan yan sandan a ranar 8 ga wata zuwa ranar 29 watannan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: