Matatar man Dangote ta fara aiki

0 185

Rahotonni sun bayyana cewa matatar mai ta Dangote wadda aka ƙaddamar tun a bara ta fara aiki a wannan Juma’ar.

Babbar matatar da ke birnin Legas ta fara aikin ne bayan kammala ta tare da ƙaddamar da ita a matsayin matatar mai mafi girma a nahiyar Afirka.

Matatar ta fara aikin ne bayan tara kimanin ganga miliyan shida na ɗanyen man fetur a wannan makon.

A watan Disambar bara ne matatar ta tabbatar da cewa ta fara karɓar ɗanyen man fetur wanda za ta fara tacewa domin samar da man fetur da sauran dangoginsa na abubuwan amfani.

A watan Nuwamba ne kamfanin mai na NNPC ya sanya hannu kan wata yarjejeniya ta samar da ɗanyen man fetur ga matatar.

Wannan dai wani lokaci ne da aka daɗe ana jira a Najeriya, ganin cewa ana sa ran matatar za ta sauya harkokin man fetur a ƙasa.

Duk da cewa Najeriya ce kan gaba wajen fitar da ɗanyen mai a Afirka, amma ba ta iya tace shi domin samar da man fetur domin amfanin cikin gida, wadda ita ce kan gaba wajen yawan jama’a da ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka. A watan Mayun 2023 ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabuwar matatar man mallakin attajirin Afirka, Aliko Ɗangote.

Leave a Reply

%d bloggers like this: